Yayin da ‘yan Najeriya ke shirin shiga bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara, Shugaban Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya ba da umurnin ƙara tsaurara matakan tsaro domin tabbatar da cewa jama’a sun yi bukukuwa cikin kwanciyar hankali.
A cewar rundunar, IGP Egbetokun ya umarci jami’an ‘yan sanda a dukkan jihohi da su ƙara yawan sintiri, kai samame a wuraren da ake zargin masu laifi ke ɓoyewa, da kuma sa ido sosai a wuraren taruwar jama’a.
Rundunar ta bayyana cewa za a mayar da hankali wajen kare wuraren ibada, kasuwanni, manyan hanyoyi, tashoshin mota da unguwanni, musamman a wannan lokaci da zirga-zirgar jama’a ke ƙaruwa.
Haka kuma, IGP Egbetokun ya bukaci jama’a da su ringa bai wa ‘yan sanda hadin kai, ta hanyar sanar da su idan sun lura da wani abu da bai dace ba, yana mai jaddada cewa tsaro aiki ne na kowa.
Rundunar ‘yan sanda ta ce wannan mataki na daga cikin shirin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da cewa lokacin bukukuwan zai kasance na farin ciki da kwanciyar hankali ga kowa.
