HomeLabarai‎‘Yansanda Sun Jaddada Ƙara Matakan Tsaro Yayin Bukukuwan Kirsimeti

‎‘Yansanda Sun Jaddada Ƙara Matakan Tsaro Yayin Bukukuwan Kirsimeti

-

‎Yayin da ‘yan Najeriya ke shirin shiga bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara, Shugaban Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya ba da umurnin ƙara tsaurara matakan tsaro domin tabbatar da cewa jama’a sun yi bukukuwa cikin kwanciyar hankali.

‎A cewar rundunar, IGP Egbetokun ya umarci jami’an ‘yan sanda a dukkan jihohi da su ƙara yawan sintiri, kai samame a wuraren da ake zargin masu laifi ke ɓoyewa, da kuma sa ido sosai a wuraren taruwar jama’a.

‎Rundunar ta bayyana cewa za a mayar da hankali wajen kare wuraren ibada, kasuwanni, manyan hanyoyi, tashoshin mota da unguwanni, musamman a wannan lokaci da zirga-zirgar jama’a ke ƙaruwa.

‎Haka kuma, IGP Egbetokun ya bukaci jama’a da su ringa bai wa ‘yan sanda hadin kai, ta hanyar sanar da su idan sun lura da wani abu da bai dace ba, yana mai jaddada cewa tsaro aiki ne na kowa.

‎Rundunar ‘yan sanda ta ce wannan mataki na daga cikin shirin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da cewa lokacin bukukuwan zai kasance na farin ciki da kwanciyar hankali ga kowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Brazil Doesn’t Necessarily Have to Win the World Cup –Vinícius

Renowned Brazilian footballer Vinícius Júnior stated that his country does not necessarily have to be among the teams that win the 2026 FIFA World Cup. He...

OMOS Continues to Fly Nigeria’s Flag High in WWE

Renowned wrestling star Omos continues to represent Nigeria on the global stage of WWE, where he stands among the tallest athletes in the world. Omos has...

Most Popular