Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta tabbatar da shirinta na karɓar Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, a wata mai zuwa, lamarin da ya fara jawo muhawara a fagen siyasar jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
Shugabannin jam’iyyar sun bayyana cewa ana dab da kammala shirye-shiryen maraba da gwamnan, inda suka ce hakan wani mataki ne na ƙarfafa APC a Plateau tare da faɗaɗa haɗin kai a tsakanin manyan ‘yan siyasa gabanin zaɓukan da ke tafe.
Wata majiya a cikin jam’iyyar ta ce zuwan Gwamna Mutfwang APC na iya sauya taswirar siyasar Plateau, musamman ganin irin tasirin da yake da shi a cikin al’umma da kuma muhimman ƙudurorin ci gaba da gwamnatinsa ke aiwatarwa.
Sai dai har zuwa yanzu, Gwamna Mutfwang bai fitar da cikakken bayani ba akan wannan shiri, duk da cewa magoya baya da masu sharhi na ci gaba da dakon lamarin.
Masana siyasa na ganin wannan mataki, idan ya tabbata, zai zama babban lamari a siyasar Arewa ta Tsakiya, tare da yiwuwar yin tasiri ga daidaiton jam’iyyun siyasa a nan gaba.
