HomeSashen Hausa‎APC Ta Shirya Karɓar Gwamnan Plateau a Wata Mai Zuwa

‎APC Ta Shirya Karɓar Gwamnan Plateau a Wata Mai Zuwa

-

‎Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta tabbatar da shirinta na karɓar Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, a wata mai zuwa, lamarin da ya fara jawo muhawara a fagen siyasar jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

‎Shugabannin jam’iyyar sun bayyana cewa ana dab da kammala shirye-shiryen maraba da gwamnan, inda suka ce hakan wani mataki ne na ƙarfafa APC a Plateau tare da faɗaɗa haɗin kai a tsakanin manyan ‘yan siyasa gabanin zaɓukan da ke tafe.

‎Wata majiya a cikin jam’iyyar ta ce zuwan Gwamna Mutfwang APC na iya sauya taswirar siyasar Plateau, musamman ganin irin tasirin da yake da shi a cikin al’umma da kuma muhimman ƙudurorin ci gaba da gwamnatinsa ke aiwatarwa.

‎Sai dai har zuwa yanzu, Gwamna Mutfwang bai fitar da cikakken bayani ba akan wannan shiri, duk da cewa magoya baya da masu sharhi na ci gaba da dakon lamarin.

‎Masana siyasa na ganin wannan mataki, idan ya tabbata, zai zama babban lamari a siyasar Arewa ta Tsakiya, tare da yiwuwar yin tasiri ga daidaiton jam’iyyun siyasa a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Dalilan Da Ya Sa Na Bar APC Na Koma ADC– Inji Wada Protocol

‎Tsohon hadimin tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, Alhaji Mustapha Abdu Saulawa, wanda aka fi sani da Wada Protocol, ya bayyana dalilin da...

Yaron Shago Ya Hallaka Ubangidansa da Almakashi a Gombe, Kwanaki Kadan Da Aurensa

Jihar Gombe ta shiga alhini biyo bayan wani mummunan lamari da ya faru a unguwar Bolari, cikin birnin Gombe, inda wani yaron shago ya kashe...

Most Popular