Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi Allah-wadai da harin bam da ya afku a wani masallaci da ke kasuwar Gamboru a Maiduguri, Jihar Borno, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu da dama.
Shettima ya bayyana cewa waɗanda suka aikata harin ba za su tsira ba, inda ya tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ƙara tsaurara matakan tsaro a jihar bayan faruwar lamarin.
A wata sanarwa da ya fitar, Mataimakin Shugaban kasar ya ce gwamnatin tarayya na tura ƙarin jami’an tsaro na musamman domin bin sawu da kama masu hannu a harin, yana mai cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron ƙasa ba.
Ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Borno da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, tare da jaddada cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da bai wa hukumomin tsaro cikakken goyon baya domin murkushe ta’addanci, musamman a yankin Arewa maso gabas.
