Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa Najeriya na ci gaba da haɗin gwiwar tsaro cikin tsari da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, domin fuskantar barazanar ta’addanci da tsattsauran ra’ayi ta hanyar amfani da tashin hankali.
Ma’aikatar harkokin waje ta bayyana hakan a ranar Alhamis, bayan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa sojojin Amurka sun kai hare-haren sama kan wuraren ‘yan ta’adda a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa, ya fitar, gwamnatin ta tabbatar da cewa harin ya haifar da “kai munanan hare-haren sama na musamman kan wuraren ‘yan ta’adda a Arewa maso yammacin Najeriya.”
Ma’aikatar ta ce wannan haɗin gwiwa da Amurka da sauran abokan hulɗa na bin ka’idojin hulɗar ƙasa da ƙasa da yarjejeniyoyin bangarori biyu, kuma ya haɗa da musayar bayanan sirri, daidaiton dabarun tsaro, da sauran tallafi da suka dace da dokokin ƙasa da ƙasa tare da mutunta ikon mulkin Najeriya.
Ebienfa ya jaddada cewa dukkan matakan yaki da ta’addanci na Najeriya suna karkata ne wajen kare rayukan fararen hula, kiyaye haɗin kan ƙasa, da kuma mutunta haƙƙi da mutuncin dukkan ‘yan ƙasa ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.
