HomeSashen HausaDA DUMI-DUMI: Bam Ya Tashi A Babbar Asibitin Jihar Kebbi

DA DUMI-DUMI: Bam Ya Tashi A Babbar Asibitin Jihar Kebbi

-

Rundunar ‘yansanda a jihar Kebbi ta tabbatar da afkuwar fashewar bam da sanyin safiyar Talata a babban asibitin Bagudo, da ke karamar hukumar Bagudo ta jihar.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Bashir Usman, ya fitar a Birnin Kebbi.

 

Usman ya ce: “Muna son tabbatar wa mazauna yankin cewa an shawo kan al’amuran tsaro gaba ɗaya bayan wata babbar kara ta fashewa da ta auku a babban asibitin Bagudo da sanyin safiyar Talata, 30 ga Disamba.

 

“Ƙungiyar tsaro ta haɗin gwiwa wadda ta ƙunshi ‘yansanda, sojoji da ‘yan sa-kai ta kulle tare da tabbatar da tsaron yankin cikin gaggawa. Ƙwararrun jami’an EOD-CBRN suna wurin suna gudanar da cikakken bincike.

 

“Muna farin cikin sanar da cewa babu wanda ya rasa ransa. Duk da cewa wani gini a bangaren ma’aikata ya lalace, mazauna wajen sun riga sun fice lafiya.

 

“Kwamishinan ‘yansanda na jihar ya ƙara tura jami’an tsaro na musamman domin tabbatar da zaman lafiya da doka.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Kwamandan NSCDC Katsina, Ya Nemi Goyon Bayan Masarautar Katsina Kan Inganta Tsoron Al’umma

Kwamandan Rundunar NSCDC a Jihar Katsina, Commandant AD Moriki, ya kai ziyara bangirma a Fadar Sarkin Katsina, inda aka sanya ma sa albarka da shawarwari...

Hukumomin Tsaro Sun Kama Mutane 8 Kan Zargin Ƙona Ofishin NSCDC a Katsina

Rundunar Tsaron NSCDC, reshen Jihar Katsina, ta kama mutane 8 da ake zargi da kai hari a Koramar Nayalli da ke Sabuwar Unguwar Katsina. ‎ ‎Hakan na...

Most Popular