Tuesday, June 16, 2026
HomeLabaraiDA DUMI-DUMI: Bam Ya Tashi A Babbar Asibitin Jihar Kebbi

DA DUMI-DUMI: Bam Ya Tashi A Babbar Asibitin Jihar Kebbi

Rundunar ‘yansanda a jihar Kebbi ta tabbatar da afkuwar fashewar bam da sanyin safiyar Talata a babban asibitin Bagudo, da ke karamar hukumar Bagudo ta jihar.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Bashir Usman, ya fitar a Birnin Kebbi.

 

Usman ya ce: “Muna son tabbatar wa mazauna yankin cewa an shawo kan al’amuran tsaro gaba ɗaya bayan wata babbar kara ta fashewa da ta auku a babban asibitin Bagudo da sanyin safiyar Talata, 30 ga Disamba.

 

“Ƙungiyar tsaro ta haɗin gwiwa wadda ta ƙunshi ‘yansanda, sojoji da ‘yan sa-kai ta kulle tare da tabbatar da tsaron yankin cikin gaggawa. Ƙwararrun jami’an EOD-CBRN suna wurin suna gudanar da cikakken bincike.

 

“Muna farin cikin sanar da cewa babu wanda ya rasa ransa. Duk da cewa wani gini a bangaren ma’aikata ya lalace, mazauna wajen sun riga sun fice lafiya.

 

“Kwamishinan ‘yansanda na jihar ya ƙara tura jami’an tsaro na musamman domin tabbatar da zaman lafiya da doka.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments