HomeSashen HausaKwamandan NSCDC Katsina, Ya Nemi Goyon Bayan Masarautar Katsina Kan Inganta Tsoron...

Kwamandan NSCDC Katsina, Ya Nemi Goyon Bayan Masarautar Katsina Kan Inganta Tsoron Al’umma

-

Kwamandan Rundunar NSCDC a Jihar Katsina, Commandant AD Moriki, ya kai ziyara bangirma a Fadar Sarkin Katsina, inda aka sanya ma sa albarka da shawarwari daga Maimartaba Sarkin Katsina, Alhaji (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman, CFR, LLD, domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro da kare rayuka da dukiyoyi.

‎Ziyarar, wadda ta gudana a Litinin 29 ga watan Disamba, 2025 a Kofar Soro, a hukumance a matsayin sabon kwamandan NSCDC na jihar, tare da neman goyon bayan masarauta don samun nasara wajen inganta tsaro da zaman lafiya.

 

Sanarwar hakan, ta fito ne daga bakin SC Buhari Hamisu, Kakakin Rundunar NSCDC ta Jihar Katsina.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, ‎Commandant Moriki ya isar da gaisuwar Babban Kwamandan NSCDC na Ƙasa, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, mni, OFR, tare da jaddada kudirin rundunar na tinkarar matsalolin tsaro a faɗin ƙasar. Ya kuma jajanta wa Sarkin Katsina kan gobarar da ta shafi wani ɓangare na fadar, tare da miƙa ta’aziyya bisa rasuwar Hakimin Ƙusada (Bebejin Katsina) da Hakimin Dutsi (Gabasawan Katsina), inda ya roƙi Allah Ya jikansu da rahama.

‎A nasa jawabin, Sarkin Katsina ya yi maraba da sabon kwamandan, yana mai jaddada muhimmancin tsaro musamman ganin halin da yankin Arewa maso Yamma ke ciki.

 

Ya yaba wa ayyukan NSCDC a Jihar Katsina, tare da ƙarfafa rundunar da ta ci gaba da jajircewa dan dorewar nasarorin da ta samu, yana mai nanata muhimmancin tattara bayanan sirri da haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki na gargajiya.

‎A ƙarshe, Sarkin Katsina ya tabbatar da goyon bayan masarautar Katsina ga dukkan hukumomin tsaro, ciki har da na farar hula, tare da yi wa Commandant Moriki addu’ar samun nasara da shiriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

DA DUMI-DUMI: Bam Ya Tashi A Babbar Asibitin Jihar Kebbi

Rundunar ‘yansanda a jihar Kebbi ta tabbatar da afkuwar fashewar bam da sanyin safiyar Talata a babban asibitin Bagudo, da ke karamar hukumar Bagudo ta...

Hukumomin Tsaro Sun Kama Mutane 8 Kan Zargin Ƙona Ofishin NSCDC a Katsina

Rundunar Tsaron NSCDC, reshen Jihar Katsina, ta kama mutane 8 da ake zargi da kai hari a Koramar Nayalli da ke Sabuwar Unguwar Katsina. ‎ ‎Hakan na...

Most Popular