HomeSashen HausaAlƙalin Alƙalai na Jihar Katsina Ya Ƙaddamar Da Bada Horo Ga Alƙalai...

Alƙalin Alƙalai na Jihar Katsina Ya Ƙaddamar Da Bada Horo Ga Alƙalai Kan Ilimin (AI) da Kafofin Yaɗa Labarai Na Zamani

-

Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Katsina ta shirya wani taron horaswa na musamman ga alƙalan majistire, domin ƙarfafa tsarin shari’a daidai da buƙatun zamani.

Taron wanda akai ma take da “Ƙarfafa Ƙwarewa kan ICT tare da Mayar da Hankali kan Basirar Wucin-Gadi ta (AI) da Sabbin Kafofin Yaɗa Labarai.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, an gudanar da taron a babban ɗakin taro na Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Katsina, a haɗin gwiwa da Gwamnatin Jihar Katsina da Kamfanin Matasa Media Links, da suka haɗa da; Jaridar Katsina Times, Katsina City News Magazine da Taskar Labarai, duk na Mallakin Malam Muhammad Danjuma Katsina.

Tunda farko, da yake buɗe taron, Alkalin Alkalai na Jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar, ya bayyana cewa, fasahar AI a yanzu ta zama muhimmin ginshiƙi a rayuwar ɗan Adam, wanda shiyasa suka ƙaddamar da ba da horo don gudanar da ayyukan Shari’a daide da zamani.

Ya gabatar da jawabinsa da cewa, taken taron, shi ne “Sabuwar Hanyar Adalci ta Hanyar Kotuna Masu Amfani da Fasahar Zamani” na nuna rawar da fasaha ke takawa wajen saurin yanke hukunci, bisa gaskiya da sauƙaƙa ayyukan kotuna.

A cewarsa, shekaru da dama da suka wuce, amfani da fasaha a kotuna abu ne da ba a ma tunani, amma a yau ICT ta zama muhimmin kayan aiki wajen adana bayanai, sadarwa, gudanar da shari’a da kuma bai wa jama’a damar samun adalci cikin sauƙi.

Haka kuma, a madadin masu shirya taron, Ahmed Abdulkadir, Darakta a Matasa Media Links, ya ce an shirya taron ne domin faɗaɗa fahimtar alƙalan majistire kan tasirin basirar wucin-gadi (AI) da sabbin kafofin yada labarai a harkar shari’a.

Ya ce sai dai, AI na iya ƙirƙirar rubuce-rubuce, hotuna, sauti da bidiyo masu kama da na gaske, lamarin da ke kawo sabbin ƙalubale a fannoni kamar hujja, sahihanci, sirri da alhakin shari’a.

Ya ƙara da cewa, manufar taron ba wai sauya alƙalai zuwa masana fasaha ba ce, sai dai gina fahimta da hikimar yanke hukunci a shari’o’in da suka shafi fasaha.

Taron ya samu halartar ƙwararrun malamai da masana, ciki har da Farfesa Mainasara Yakubu Kurfi daga Sashen Ilimin Aikin Jarida na Jami’ar Bayero, Kano. Ya gabatar da takarda mai taken “Shari’a a Zamanin Kafofin Sadarwar Zamani”, inda ya ja hankalin alƙalai kan amfani da kafofin sada zumunta cikin ladabi, ƙa’ida da kiyaye mutuncin ofishinsu.

A jawabin sa na maraba, Babbar Magatakardar Kotun Jihar Katsina, Hajiya Basira, ta yaba wa Alkalin Alkalai bi sa amincewa da shirya taron, tare da jinjina wa alƙalan majistire kan ƙoƙarinsu na ƙara ilimi da ƙwarewa. Ta bayyana taron a matsayin muhimmin shiri da zai taimaka wajen inganta ayyukan kotuna a jihar.

Maharta taron sun bayyana jin daɗinsu da irin ilimin da suka samu, inda suka jaddada cewa horon zai taimaka musu wajen fuskantar ƙalubalen shari’o’in da suka shafi fasaha da sabbin kafofin yada labarai.

Taron ya nuna ƙudirin Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Katsina na ci gaba da gina ƙwarewar alƙalai, amfani da fasaha cikin gaskiya, da kuma shirin tunkarar ƙalubalen shari’a a zamanin basirar wucin-gadi da kafofin sadarwa na zamani da ke taka rawa na wannan karni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

An Zaɓi Hon. Dauda Kurfi A Matsayin Shugaban Ƙungiyar Tsofaffin Kansiloli A Jihar Katsina

Tsofaffin Kansiloli, sun rushe shugabancin ƙungiyar tsofaffin Kansilolin ta ƙasa reshen jihar Katsina, inda suka zaɓi Hon. Dauda Kurfi, a matsayin shugaban ƙungiyar tsofaffin Kansiloli...

Dikko Radda Ya Amince Da Naɗin Sabbin Manyan Sakatarori a Jihar Katsina

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya amince da naɗin sabbin manyan sakatarorin jihar.   Gwamnan ya ce an gudanar da naɗin bi sa cancanta da...

Most Popular