Gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 1.07 domin gyaran gidajen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima a kasafin kuɗin 2026, lamarin da ya sanya adadin kuɗin da aka ware don gyaran gidajen su cikin shekara uku ya kai Naira biliyan 18.4, in ji rahoton Daily Trust.
Haka kuma, Hukumar EFCC, wadda kuɗinta ke ƙarƙashin sashen fadar shugaban kasa a kasafin, ta shirya kashe Naira biliyan 3.2 a bana domin tsaftace ofisoshinta da da kuma abinci da kayan shakatawa.
Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗi na 2026 a w zaman haɗin gwiwar Majalisar Tarayya a ranar 19 ga Disamba.
A baya, ya rubuta wa Majalisar Dattawa da ta Wakilai wasiƙa yana neman sake aiwatar da dokar kasafin kuɗi ta shekarar 2024 da kuma ta shekarar 2025, inda yawan kuɗaɗen kashewa ya kai Naira tiriliyan 43.56 da tiriliyan 48.32, domin tabbatar da cikar aiwatar da su kafin 31 ga watan Maris, na shekarar 2026.
Kudirin kasafin kuɗi na yanzu yana ɗauke da jimillar kashe kuɗi Naira tiriliyan 58.18, wanda ya haɗa da Naira tiriliyan 15.52 don biyan bashin cikin gida da na waje. Ana sa ran samun kuɗaɗen shiga na Naira tiriliyan 34.33, wanda ke barin gibi na Naira tiriliyan 23.85 da za a rufe ta hanyar ɗaukar bashi daga cikin gida da kuma ƙasashen waje.
