Wata mata mai suna Aishatu Umar, mazauniyar Jihar Kano, ta rasu da misalin ƙarfe 1:00 na dare bayan shafe tsawon watanni tana fama da matsanancin ciwon ciki, sakamakon abin da ake zargin sakacin likitoci yayin aikin tiyata.
Rahotanni sun nuna cewa an yi wa marigayiyar tiyata ne a Abubakar Imam Urology Center a watan Satumba da ya gabata, Bayan kammala tiyatar, Aishatu ta cigaba da fama da matsanancin ciwon ciki, inda duk lokacin da ta koma asibiti, aka rika bata magungunan rage zafi kawai ba tare da gano ainihin matsalar ba.
Bayan shafe kusan watanni huɗu tana wahala, kwana biyu kafin rasuwarta ne aka yi mata gwaje-gwaje da hoton CT scan, inda aka gano cewa an manta almakashi (scissors) a cikin cikinta tun lokacin da aka yi mata tiyatar farko.
Rahotanni sun kara da cewa an shirya a yi mata wata gyaran tiyata domin cire kayan da aka bari a cikinta, sai dai abin takaici, kafin a aiwatar da hakan, marigayiyar ta rasu.
Marigayiyar Aishatu Umar ta bar miji da ’ya’ya biyar, lamarin da ya jefa iyalanta da al’umma cikin alhini da jimami.
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, inda da dama ke kallon faruwar al’amarin a matsayin sakaci mai tsanani daga bangaren ma’aikatan lafiya, tare da bukatar a hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Al’umma da iyalan marigayiyar sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da hukumomin kula da harkokin lafiya da su gaggauta gudanar da bincike mai zurfi, tare da ɗaukar matakin da ya dace domin tabbatar da adalci ga Aishatu Umar da kuma hana afkuwar irin wannan lamari a nan gaba.
