HomeSashen HausaKashe Waɗanda Suka Hallaka Uwa Da ’Ya’yanta a Kano Ya Saɓa Wa...

Kashe Waɗanda Suka Hallaka Uwa Da ’Ya’yanta a Kano Ya Saɓa Wa Dokokin Najeriya— Babba Lauya a Kano

-

Wani babban Lauya a Kano ya yi gargadi kan kiran da ake na gaggauta hukuncin kisa kaitsaye ga waɗanda aka kama a Dorayi-Chiranci.

‎Shahararren lauya a Jihar Kano, Mubarak Abubakar, ya bayyana cewa kiran da ake yi na gaggauta kashe wadanda ake zargi da kisan wata uwa da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi-Chiranci, ba daidai ba ne kuma ya saba wa tsarin shari’ar laifuka na Najeriya.

Kamar yadda Nigerian Post ta bibiyi Rahotan a Aminiya, ‎a cikin wata sanarwa da ya fitar, Lauyan ya yi nuni cewa, kowa na da haƙƙin samun adalci ta hanyar shari’a kafin a yanke ma sa hukunci, kuma kiran da jama’a ke yi na gaggauta hukunci na iya kawo matsala ga tsarin shari’a da kuma hana adalci ga wadanda ake zargi.

‎Mubarak Abubakar ya ƙara da cewa, duk wanda ake zargi da laifi dole ne a bi doka da oda. Duk wani hukunci da aka yanke kafin bincike da shari’a cikakke, zai zama abin ƙalubalanta a doka kuma zai saba wa tsarin dimokuradiyya.

Haka kuma, ‎Lauyan ya bukaci jami’an tsaro da al’umma da su bar shari’a tayi aiki yadda ya kamata, tare da yin hakuri yayin da kotu ke gudanar da bincike kan lamarin.

Sai dai kuma, ‎har yanzu ba a bayyana ranar fara shari’ar waɗanda ake zargin ba, amma jami’an tsaro sun tabbatar da cewa, suna ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin don tabbatar da adalci ga duka bangarorin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Dalilan Da Ya Sa Na Bar APC Na Koma ADC– Inji Wada Protocol

‎Tsohon hadimin tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, Alhaji Mustapha Abdu Saulawa, wanda aka fi sani da Wada Protocol, ya bayyana dalilin da...

Yaron Shago Ya Hallaka Ubangidansa da Almakashi a Gombe, Kwanaki Kadan Da Aurensa

Jihar Gombe ta shiga alhini biyo bayan wani mummunan lamari da ya faru a unguwar Bolari, cikin birnin Gombe, inda wani yaron shago ya kashe...

Most Popular