A lokacin murnar tunawa da bikin na shekara-shekara, kungiyar ta yi kira gameda samar da haɗin Kai, muhalli mai dadin amfani, mutunta juna da daidaitattun damarmaki ga Masu Bukata ta Musamman a bangaren rashin gani.
Katsina Post ta bibiyi cewa, a yayin bikin tunawa da Ranar Tsaron Amfani da Sandar Farar Makafi ta Duniya (International White Cane Safety Day), Ƙungiyar Katsina Blind Children Intellectual Club ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ƙara himma wajen kare haƙƙoƙi, mutunci, ‘yancin kai, tsaro da kuma tabbatar da cikakken shigar makafi da masu matsalar gani cikin harkokin al’umma.
Tunda farko, Ƙungiyar ta miƙa wannan saƙo ga gwamnati da masu tsara manufofin jihar Katsina, ƙungiyoyin farar hula (CSOs), ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGOs), ‘yan siyasa, shugabannin addinai, sarakunan gargajiya da sauran al’umma baki ɗaya.
Hakan na kunshe ne a wata takarda da shugaban Ƙungiyar, Katsina Blind Children Intellectual Club (KBCIC), Comrade Nasir Dauda Yansiliyu, ya sanya wa hannu tare da rabawa Manema Labarai, ranar Alhamis 15 ga watan Oktoba 2026.
A cewar saƙon, sandar makafi alama ce ta ‘yancin kai, zirga-zirga, ƙarfin gwiwa da kuma walwala ga mutanen da ke fama da matsalar rashin gani.
Saboda haka, ƙungiyar ta buƙaci haɗin gwiwar kowa wajen gina al’umma da kowane mutum zai iya zirga-zirga cikin sauki, samun ilimi, samun aikin yi, shiga harkokin shugabanci da kuma more daidaitattun damarmaki ba tare da nuna wariya ba.
Haka kuma, ya jaddada muhimmancin samar da muhallin da za su rinka amfani da su a matsayin mallakin Masu Bukata ta Musamman, inganta ilimin da ya haɗa kowa, samar da damarmakin aikin yi da kuma mutunta haƙƙoƙin masu buƙata ta musamman.
Haka kuma, ya bayyana cewa, haɗa Masu Bukata ta Musamman cikin al’umma haƙƙine ga shugabacin, ba wata sadaka ko taimakon alkhairi da ake yi musu ba.
Ya kuma jaddada taken masu fafutukar kare haƙƙin Masu Bukata ta Musamman mai cewa; “Babu abin da ya shafe mu da za a yi ba tare da shigar mu ba!”
A ƙarshe, shugaban ƙungiyar ya yi kira ga al’umma da su haɗa kai wajen kawar da shingayen da ke hana Masu Bukata ta Musamman samun ci gaba, yaƙi da nuna wariya da kuma gina al’umma da za ta amince da ƙwarewa, baiwa da kuma irin gudunmawar da Masu Bukata ta Musamman musamman a bangaren masu matsalar gani za su iya bayarwa.
