An kama wasu matasa biyu a yankin Obodogba da ke Okpanam, kusa da birnin Asaba, a Jihar Delta ta Najeriya, bisa zargin ƙoƙarin bínne gàwar wata ƙàramàr yarínya a cikin yanayin da har yanzu hukumomi ba su fayyace ba.
Lamarin ya jawo hankalin mazauna yankin bayan an gano abin da ke faruwa a ranar Talata, inda wasu daga cikin jama’ar yankin suka shiga tsakani tare da hana waɗanda ake zargin ci gaba da bínne gàwar yar8nyar.
Rahotanni sun bayyana cewa, bayan gano lamarin, mazauna yankin sun tilasta wa waɗanda ake zargin tóno gawar daga inda ake ƙoƙarin bínne ta. Daga bisani, an miƙa mutanen ga rundunar ’yan sandan jihar domin gudanar da bincike kan lamarin.
Wannan lamari ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, musamman bayan bayyanar wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ya nuna yadda wasu matasa suka taru a wajen lamarin.
A cikin bidiyon, an ga wasu matasa na rakiyar waɗanda ake zargin, yayin da wasu daga cikin mutanen da suka taru suka riƙa dukansu. Sai dai wasu daga cikin mahalarta taron sun yi kira da a miƙa waɗanda ake zargin ga ’yan sanda domin gudanar da bincike da kuma ɗaukar matakin da ya dace bisa doka.
Rahoton da Nigerian Post ta bibiya daga kafar SaharaReporters ya nuna cewa, duk da yadda lamarin ya tayar da hankalin jama’a, har yanzu akwai muhimman bayanai da ba a tabbatar da su ba game da abin da ya faru da yarínyar.
Kafin hada wannan rahoton, ba a tabbatar da musabbabin mutuwar yarinyar ba, tare da yunkurin bínneta da matasan suke shirin yi.
Ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto, ba a bayyana a hukumance musabbabin mutuwar ƙaramar yarinyar ba. Haka kuma, ba a tabbatar da dalilin da ya sa waɗanda ake zargin suka yi ƙoƙarin binne gawarta a lokacin da lamarin ya faru ba.
Haka nan, babu wani cikakken bayani daga hukumomi da ya tabbatar da yanayin da yarinyar ta mutu ko kuma abin da ya faru kafin a gano gawarta.
Wannan ya sa ake jiran sakamakon binciken ’yan sanda domin gano ainihin abin da ya faru, da kuma ko akwai wani laifi da aka aikata da ya danganci mutuwar yarinyar ko ƙoƙarin binne gawarta.
Da take neman ƙarin bayani kan lamarin, kafar SaharaReporters ta tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Delta, SP Bright Edafe.
Sai dai jami’in ya bayyana cewa rundunar ’yan sandan ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba a lokacin da aka tuntube shi.
Wannan na nufin har yanzu ana buƙatar ƙarin bayani daga hukumomin tsaro domin tabbatar da cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru, tare da fayyace matakan da aka ɗauka bayan kama matasan biyu.
Haka kuma, zargin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa an yi wa yarinyar lalata bai samu tabbaci daga wata sanarwa ta hukuma ko wata sahihiyar hujja da aka gabatar ba.
Haka nan, bayanin da ake dangantawa da ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin game da mutuwar yarinyar bai samu tabbaci daga hukumomin da abin ya shafa ba.
A halin yanzu, ana jiran ƙarin bayani daga rundunar ’yan sandan Jihar Delta domin tabbatar da ainihin abin da ya faru da yarinyar, yanayin mutuwarta da kuma dalilin da ya sa aka yi ƙoƙarin binne gawarta.
Ana kuma sa ran binciken zai taimaka wajen gano ko akwai wasu bayanai ko mutanen da suke da alaƙa da lamarin, da kuma matakin shari’a da ya dace a ɗauka kan waɗanda aka kama idan aka tabbatar da aikata wani laifi.
Ya kamata a lura cewa, kama mutum bisa zargi ba yana nufin an tabbatar da laifinsa ba. Saboda haka, ya dace a bar hukumomin da ke gudanar da bincike su gano gaskiyar lamarin, tare da tabbatar da cewa duk wani mataki da za a ɗauka ya dace da tanadin doka.
Nigerian Post za ta ci gaba da bibiyar lamarin tare da kawo ƙarin bayani idan hukumomin da abin ya shafa suka fitar da wata sanarwa a hukumance.
