Dantakarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADP, Amb. Aliyu Ibn Abbas, ya ce ba zai goyi bayan sauran ’yan takarar da ake kira su haɗa kai domin kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 ba, yana mai cewa akwai shari’o’in kotu da za su iya shafar makomar takarar wasu daga cikinsu.
Aliyu Ibn Abbas ya bayyana cewa, idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027, zai yi shugabanci bisa tsarin marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua, tare da ƙara manufar haɗin kan ’yan Najeriya domin magance rabuwar kai a ƙasar.
Ya ce yana goyon bayan manufofi bakwai na gwamnatin Yar’Adua, inda ya bayyana cewa zai ƙara manufar haɗin kan ƙasa domin su zama manufofi takwas.
Dangane da batun tallafin man fetur, ɗan takarar ya bayyana cewa akwai buƙatar nazarin ra’ayoyin jama’a kafin yanke kowace shawara dan sanin yiyuwar za a dawo da tallafin ko a’a.
Ya ce jam’iyyarsa na tattara ra’ayoyin al’umma kan wasu tsare-tsare, ciki har da batun tallafin man fetur, domin ɗaukar matakin da zai fi amfani ga ’yan Najeriya.
A cewarsa, cire tallafin man fetur ya kasance cikin alkawuran da manyan ’yan takarar shugaban ƙasa suka yi a zaɓen 2023, ciki har da Bola Tinubu, Atiku Abubakar da kuma Peter Obi.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, kan batun haɗa kan ’yan takara domin fuskantar Tinubu a 2027, Aliyu Ibn Abbas ya ce bai kamata a janye takara domin mara wa wani ɗan takara baya ba tare da la’akari da shari’o’in da ke gaban kotu ba.
Ya yi tambaya kan makomar siyasar Arewa idan ’yan takarar suka janye wa mutum ɗaya, daga bisani kuma hukuncin Kotun Ƙoli ya shafi cancantar takararsa.
Ya ƙara da cewa yana da tsare-tsare da suka shafi tsaro, inganta kiwon lafiya da ilimi, samar da ayyukan yi ga matasa, kyakkyawan shugabanci da bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.
A ƙarshe, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ba matasa dama domin su nuna ƙwarewarsu da gudummawar da za su iya bayarwa wajen ci gaban ƙasa.
