Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta kama wasu mutum huɗu da ake zargi da satar kayan aikin layin dogo, tare da ƙwato sandunan shimfiɗar layin dogo guda 70 da aka ɓoye a bayan buhunan abincin dabbobi guda 17.
Nigerian Post ta bibiyi rahoton da The Channels cewa, an kama waɗanda ake zargin ne a ranar 11 ga Oktoba, 2026, bayan jami’an ’yan sanda sun tare wata mota kirar J5, Fara a kan hanyar Kurfi zuwa ƙauyen Tsanni, yayin gudanar da binciken ababen hawa.
Rundunar ’yan sandan ta ce binciken farko ya nuna cewa ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya ambaci wani mutum daga Jihar Bauchi a matsayin wanda ake zargin yana samar musu da kayan, wanda har yanzu yake tsere.
Rahotanni sun ce ana jigilar kayan aikin da aka sace ne domin kai su ga wani mutum a cikin garin Katsina.
Rundunar ta bayyana cewa tana ci gaba da tsare waɗanda aka kama, yayin da ake ƙoƙarin cafke wanda ya tsere tare da gano wurin da aka lalata kayayyakin layin dogon domin sace sandunan.
