Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau, ta kori wani ɗan agajinta bayan bayyanarsa a wani bidiyo yana barazanar kai hare-hare a jihohin Enugu da Plateau.
NIGERIAN POST ta bibiyi cewa, Babban Daraktan Agajin ƙungiyar na ƙasa, Injiniya Mustapha Imam Sitti, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026.
Sanarwar ta ce an ɗauki matakin korar mutumin ne bayan gudanar da binciken ladabtarwa a kansa, tare da jaddada cewa mutumin ba ya cikin mambobin ƙungiyar a halin yanzu.
Ƙungiyar ta bayyana cewa kalaman da mutumin ya yi a cikin bidiyon ba sa wakiltar matsayinta, akidarta ko manufofinta, tana mai nesanta kanta da duk wani furuci da zai iya haifar da tashin hankali ko barazana ga zaman lafiyar al’umma.
Haka kuma, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi kira ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin gano hakikanin abin da ya faru tare da ɗaukar matakan da suka dace.
Sanarwar ta kuma buƙaci jama’a da su kwantar da hankulansu, su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, tare da bai wa hukumomin tsaro damar gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Ƙungiyar ta jaddada muhimmancin kiyaye zaman lafiya da bin doka, musamman a lokutan da ake samun bayanai da za su iya haddasa fargaba ko tayar da hankalin jama’a.
