Gwamnatin tarayya ta bukaci Majalisar Tarayya da ta dakatar da duba tare da amincewa da kudirorin kafa sabbin jami’o’in gwamnati, kwalejojin kimiyya da fasaha da kuma kwalejojin horas da malamai.
Ministan Ilimi, Dr. Maruf Alausa, ne ya bayyana hakan cikin wata wasika da ya aikewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, inda ya bukaci a aiwatar da dokar dakatar da kafa sabbin manyan makarantun gwamnati na tsawon shekaru bakwai.
Alausa ya ce matakin, wanda Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da shi a ranar 13 ga Agustan 2025, ya zama dole domin rage matsalolin karancin kudade da inganta harkokin ilimi a makarantun da ake da su.
Ya bayyana cewa jami’o’i da sauran manyan makarantun gwamnati na fuskantar matsalolin karancin malamai, dakunan karatu, dakunan gwaje-gwaje, masauki da kuma lalacewar kayayyakin more rayuwa.
Ministan ya ce maimakon kafa sabbin makarantu, ya kamata gwamnati ta mayar da hankali wajen inganta wadanda ake da su, ta hanyar samar da isassun kudade, kayan aiki da kwararrun ma’aikata.
Ya kuma bayyana cewa daga cikin Naira tiriliyan 1.3 da gwamnati ta yi alkawarin warewa domin farfado da jami’o’i tsakanin 2013 zuwa 2018, Naira biliyan 250 ne kawai aka saki tsakanin 2013 zuwa 2021.
Haka kuma, ya ce daga cikin Naira biliyan 150 da aka amince da su a shekarar 2025 domin tallafa wa jami’o’i, Naira biliyan 50 ne aka fara fitarwa.
Alausa ya yi gargadin cewa kafa sabbin makarantu ba tare da cikakken shirin samar da kudade da kayayyakin aiki ba, na iya haifar da makarantu da za su kasance a takarda kawai ba tare da karfin gudanar da ingantaccen karatu ba.
Ya bukaci ‘yan majalisar da su fifita ingancin ilimi da dorewar makarantun da ake da su maimakon ci gaba da kara yawan manyan makarantun gwamnati.
