Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ƙarin da aka samu na wasu rumfunan zaɓe ya samo asali ne daga hukuncin kotu da ya haifar da ƙirƙirar sabbin mazaɓu a jihohin Kogi, Benue da Delta.
Hakan na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta ƙara rumfunan zaɓe 453, lamarin da ya sa adadinsu ya tashi daga 176,846 zuwa 177,299 a faɗin ƙasar.
Sai dai, Nigerian Post ta bibiyi cewa hukumar ba ta tabbatar da sahihancin wannan sabon adadi ba, inda ta ce za ta yi wa masu ruwa da tsaki cikakken bayani kan lamarin bayan kammala binciken da take gudanarwa.
Haka kuma, hukumar na fuskantar tambayoyi dangane da zargin amfani da hotunan bogi da aka samar ta hanyar fasahar basirar na’ura (AI) a yayin rajistar masu zaɓe.
INEC dai na buƙatar fayyace wa al’umma ƙarin bayanai kan waɗannan batutuwa domin tabbatar da gaskiya da kuma kawar da duk wani shakku game da sahihancin tsarin rajistar masu zaɓe.
