Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama wasu mutane takwas bisa zargin lalatawa da satar kayan more rayuwa na gwamnati da na masu zaman kansu.
Mai magana da yawun rundunar, Josephine Adeh, ta ce an kama mutanen ne yayin wani sintirin yaƙi da laifuffuka da aka gudanar da misalin ƙarfe 3:00 na dare ranar 23 ga Oktoba.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Waɗanda aka kama sun haɗa da Sani Musa, Ashiru Adamu, Markus Joseph, Suleman Ibrahim, Jamilu Umar, Usman Aliyu, Uzairu Sani da Shafiu Bala.
Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin mambobi ne na wata ƙungiyar masu aikata laifuffuka da ta ƙware wajen lalatawa da satar kayan more rayuwa a Abuja, musamman a Central Business District, Maitama, Wuse, Garki da Asokoro.
Rundunar ta ce ta kwato dogayen sandunan fitilun titi guda biyar da ake zargin an sace bayan an yanke su daga inda aka dasa su.
A cewar rundunar, ana ci gaba da tsare waɗanda ake zargin da kayayyakin da aka kwato, yayin da za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.
