An Zargi Tsohuwar Ma’aikaciyar Jaiz Bank da Damfarar Kwastomomi Miliyan 104 a Jos
Wata tsohuwar ma’aikaciyar Jaiz Bank mai suna Habiba Abdulrahman, mai shekaru 35, na fuskantar zargin damfarar wasu kwastomomin bankin su 12 kuɗaɗen da yawansu ya kai naira miliyan 104 a birnin Jos na Jihar Plateau.
Rahoton binciken rundunar ’yan sandan jihar Plateau ya nuna cewa Habiba, wadda ta taɓa riƙe muƙamin shugabar ayyukan bankin (Operations Head), ta riƙa karɓar kuɗaɗen kwastomomi da sunan saka musu a asusun ajiyar kuɗi na musamman (Fixed Deposit), alhali ba ta buɗe irin waɗannan asusu ba.
An zarge ta da amfani da takardun bankin da aka ƙirƙira da kuma sa hannun bogi wajen yaudarar kwastomomin, tare da karkatar da kuɗaɗen zuwa asusun mijinta, Manir Murtala, da ƙanwarta, Zainab Abdulrahman.
’Yan sanda sun ce sun gano takardun cire kuɗi da takardun shaidar ajiyar kuɗi na bogi a gidan wadda ake zargin, inda bincike ya nuna cewa babu wani sahihin asusun ajiyar kuɗi da aka buɗe wa waɗanda abin ya shafa.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Rahoton ya kuma bayyana cewa Habiba ta amsa cewa ta damfari kwastomomin, tare da cewa ta saka kuɗaɗen a harkar haƙar ma’adinai, amma ba a samu hujjar tabbatar da hakan ba.
Binciken ya kuma nuna cewa an kori Habiba daga aiki a watan Janairun 2026 bayan bankin ya gano wasu kura-kurai. Daga bisani ’yan sanda suka kama ta, inda suka tsare ta na tsawon makonni biyu kafin a ba ta belin lafiya.
A halin yanzu, kwastomomin da abin ya shafa sun gudanar da zanga-zanga a gaban bankin a Jos, suna neman a mayar musu da kuɗaɗensu.
Sai dai lauyan bankin, Munir Barau, ya ce kwastomomin sun yi mu’amala ne da tsohuwar ma’aikaciyar kai tsaye, ba da bankin ba, yana mai cewa wasu daga cikinsu sun yi cinikin ne bayan lokutan aiki har ma a gidanta.
Rahoton ya ce har yanzu ba a tabbatar ko an gurfanar da Habiba da mutanen da ake zargin sun taimaka mata a gaban kotu ba.
Sai dai, Habiba ta shaida wa wakilin jaridar cewa za ta dawo da nata bayanin kan lamarin nan gaba.
