Wasu matasa da ake zargin ’yan daba ne sun kai hari tare da kawo cikas ga gangamin siyasar ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Lamarin ya faru ne ranar Laraba, lokacin da Pantami ke kan hanyarsa ta shiga birnin Gombe domin halartar gangamin siyasa da jam’iyyar PDP ta shirya domin yi masa maraba, bayan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta wallafa sunansa a matsayin ɗan takararta.
Shaidu sun bayyana cewa matasan sun tare hanyar Jekadafari, kusa da gidan iyalan Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, inda suka tara tayoyi suka cinna musu wuta, lamarin da ya haddasa hayaƙi mai yawa tare da firgita masu ababen hawa da mazauna yankin.
Rahotanni sun ce wasu daga cikin matasan sun kuma farfasa gilasan motocin da ke cikin ayarin motocin Pantami, yayin da ake zargin suna ɗauke da makamai masu haɗari.
Sai dai ayarin motocin Pantami, wanda ya ƙunshi ɗaruruwan motoci, ya samu damar wucewa tare da ci gaba da tafiya zuwa wurin taron.
Daga bisani jami’an tsaro da aka tura yankin sun shiga tsakani tare da dawo da zaman lafiya.
A lokacin da aka haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar Gombe da kuma Pantami ba su fitar da sanarwar hukumance kan lamarin ba.
A nasa jawabin yayin taron da aka gudanar a fadar Sarkin Gombe, Pantami ya yi kira ga al’ummar jihar da su guji zaɓen ’yan siyasar da yake zargi da kallon dukiyar jihar a matsayin ganimar siyasa.
Ya ce dukiyar Gombe mallakin al’ummar jihar ce, yana mai cewa shirinsa shi ne samar da ayyukan yi, tallafa wa matasa da manoma, da kuma samar da takin zamani domin bunƙasa noma.
Tsohon gwamnan jihar kuma jagoran PDP, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, ya gode wa magoya bayan jam’iyyar bisa halartar taron, yayin da shugaban PDP na ƙasa, Abdurrahman Muhammad, ya yi kira ga ’ya’yan jam’iyyar da su haɗa kai domin ƙarfafa jam’iyyar a jihar.
