Rundunar Civil Defence (NSCDC) ta kama wani mutum mai shekaru 55, Monday Williams, bisa zargin lalatawa da satar wayoyin sadarwa a kan hanyar Kugbo zuwa Nyanya da ke Abuja.
Hukumar ta ce ta kama wanda ake zargin ne yayin sintiri, bayan samun bayanan sirri, inda jami’anta suka tarar da shi a cikin ramin wayoyin sadarwa yana cire su.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, An ƙwato naɗaɗɗun wayoyin sadarwa guda biyu masu tsawon kimanin mita 3,000 daga hannunsa.
Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Demsa ne a Jihar Adamawa, kuma ya taɓa aiki a fannin girka wayoyin sadarwa tun shekarar 2004.
Ya kuma ambaci wani mutum mai suna Emeka a matsayin wanda yake hulɗar aiki da shi, wanda hukumar ke nema domin bincike.
Kwamandan NSCDC na Abuja, Olusola Odumosu, ya yi gargaɗin cewa lalata kadarorin sadarwa na kawo cikas ga harkokin jama’a da kasuwanci, yana mai jaddada cewa hukumar ba za ta lamunci irin waɗannan laifuka ba.
