Monday, November 16, 2026
HomeLabarai'Yan Sanda Sun Kama ’Yan Kano 2 Bisa Zargin Hallaka Mai Babur...

‘Yan Sanda Sun Kama ’Yan Kano 2 Bisa Zargin Hallaka Mai Babur a Rivers

Rundunar ’yan sandan Jihar Rivers ta kama wasu matasa biyu ’yan asalin Jihar Kano bisa zargin kashe wani mai babur ɗan Jihar Jigawa, tare da gano gawarsa a cikin wani daji da ke Ƙaramar Hukumar Ahoada West ta jihar.

Rundunar ta ce waɗanda ake zargin, Abubakar Sani mai shekaru 24 da Yusuf Magaji mai shekaru 20, sun yaudari marigayin mai suna Sani Musa, ɗan garin Zago da ke Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa a Jihar Jigawa, zuwa wani daji a garin Mbiama, inda suka daba masa wuƙa har ya mutu, sannan suka ɓoye gawarsa suka sace babur ɗinsa.

’Yan sandan sun kama su ne a ranar 22 ga Oktoba, 2026, a Choba Motor Park, lokacin da ake zargin suna ƙoƙarin wargaza babur ɗin da suka sace.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun amsa aikata laifin, tare da bayyana cewa sun shirya tura babur ɗin zuwa Jihar Kano ta hanyar jigilar kaya.

Daga bisani, sun jagoranci jami’an ’yan sanda zuwa dajin da suka ɓoye gawar, inda aka gano ta tare da sanar da iyalan marigayin domin gudanar da jana’izarsa bisa tsarin addinin Musulunci.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Olugbenga Adewole Adepoju, ya bayar da umarnin zurfafa bincike domin gano ko akwai wasu da ke da hannu a kisan tare da gurfanar da duk waɗanda aka samu da laifi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments