Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da wasu gwamnonin APC da kokarin dakile jam’iyyun adawa gabanin zaben 2027.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye dalibai karo na biyar na Jami’ar Skyline da ke Kano, inda ya nuna damuwa kan cire sunayen dan takarar gwamnan Kano na NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, da mataimakinsa, Mustapha Kwankwaso, daga jerin sunayen ‘yan takarar da INEC ta fitar.
Ya ce dan takarar da mataimakinsa sun cika dukkan sharuddan tsayawa takara, kuma INEC ta amince da takararsu tun farko kafin daga bisani ta cire sunayensu.
A cewarsa, INEC ta bayyana cewa ta cire sunayen ne bisa umarnin kotu, duk da cewa an samu umarnin ne kwanaki 19 bayan hukumar ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar a ranar 10 ga Oktoba.
Kwankwaso ya ce jam’iyyar ta rubuta wa hukumar domin neman karin bayani, sannan shugabannin NDC na kasa suka nemi a mayar da shari’ar zuwa Babbar Kotun Tarayya.
Haka kuma, ya zargi wasu gwamnonin APC da amfani da jami’an tsaro da ‘yan daba wajen hana jam’iyyun adawa gudanar da gangamin siyasa, musamman a jihohin Benue, Legas da Cross River.
Ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da adalci tare da kare dimokuradiyyar kasar.
A wani bangare na bikin, mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Ajith Kumar V.V. Kumar, ya ce jami’ar ta yaye dalibai 236 a zangon karatu na 2025/2026.
Ya ce daga cikinsu, 183 sun kammala digiri na farko, 41 sun kammala digiri na gaba, yayin da 12 suka samu digirin digirgir (PhD).
Ya kara da cewa dalibai 30 sun samu matakin digiri na farko (First Class), yayin da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta amince da karin kwasa-kwasai uku da suka hada da Ilimin Kiwon Lafiyar Jama’a, Tattalin Arziki da Kudi na Musulunci da kuma Fasahar AI (Artificial Intelligence) Ya Zargi INEC da Kokarin Hana NDC Takarar Gwamnan Kano
Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da wasu gwamnonin APC da kokarin dakile jam’iyyun adawa gabanin zaben 2027.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye dalibai karo na biyar na Jami’ar Skyline da ke Kano, inda ya nuna damuwa kan cire sunayen dan takarar gwamnan Kano na NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, da mataimakinsa, Mustapha Kwankwaso, daga jerin sunayen ‘yan takarar da INEC ta fitar.
Ya ce dan takarar da mataimakinsa sun cika dukkan sharuddan tsayawa takara, kuma INEC ta amince da takararsu tun farko kafin daga bisani ta cire sunayensu.
A cewarsa, INEC ta bayyana cewa ta cire sunayen ne bisa umarnin kotu, duk da cewa an samu umarnin ne kwanaki 19 bayan hukumar ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar a ranar 10 ga Oktoba.
Kwankwaso ya ce jam’iyyar ta rubuta wa hukumar domin neman karin bayani, sannan shugabannin NDC na kasa suka nemi a mayar da shari’ar zuwa Babbar Kotun Tarayya.
Haka kuma, ya zargi wasu gwamnonin APC da amfani da jami’an tsaro da ‘yan daba wajen hana jam’iyyun adawa gudanar da gangamin siyasa, musamman a jihohin Benue, Legas da Cross River.
Ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da adalci tare da kare dimokuradiyyar kasar.
A wani bangare na bikin, mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Ajith Kumar V.V. Kumar, ya ce jami’ar ta yaye dalibai 236 a zangon karatu na 2025/2026.
Ya ce daga cikinsu, 183 sun kammala digiri na farko, 41 sun kammala digiri na gaba, yayin da 12 suka samu digirin digirgir (PhD).
Ya kara da cewa dalibai 30 sun samu matakin digiri na farko (First Class), yayin da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta amince da karin kwasa-kwasai uku da suka hada da Ilimin Kiwon Lafiyar Jama’a, Tattalin Arziki da Kudi na Musulunci da kuma Fasahar AI (Artificial Intelligence).
