Tuesday, November 17, 2026
HomeLabaraiTinubu Ya Yi Wa Mutane 78 Da Aka Kama Kan Jifar Ayarinsa...

Tinubu Ya Yi Wa Mutane 78 Da Aka Kama Kan Jifar Ayarinsa Afuwa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin sakin mutane 78 da aka kama bisa zargin hannu a harin da aka kai wa ayarinsa a Abuja ranar Juma’a.

Kakakin rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin.

Ta ce an kama mutanen ne bayan wasu fusatattun matasa sun yi wa ayarin motocin shugaban ƙasa ruwan duwatsu da wasu abubuwa masu haɗari, jim kaɗan bayan ya kammala sallar Juma’a a wani masallaci da ke unguwar Garki a Abuja.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Sanarwar ta bayyana cewa harin ya yi sanadin lalacewar wasu motoci tare da jikkata jami’an tsaro.

Rundunar ’yan sandan ta ce bayan kama mutanen, fadar shugaban ƙasa ta bayar da umarnin yi musu gargaɗi tare da sake su bisa afuwar da shugaban ƙasa ya yi musu.

Ta ƙara da cewa a halin yanzu ana gudanar da shirye-shiryen sakin waɗanda aka kama.

Kwamishinan ’yan sandan Abuja, Ahmed Mohammed Sanusi, ya yi gargaɗin cewa rundunar ba za ta lamunci tashin hankali da lalata dukiyoyin jama’a ba, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.

Ya kuma buƙaci mazauna Abuja su kasance masu sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga jami’an tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments