Uwargidan Gwamnan Jihar Kano, Hajiya Maryam Abba Kabir Yusuf, ta ƙaddamar da shirin rabon fakitin audugar mata guda 10,000 ga ɗalibai mata a makarantun kwana da na je ka ka dawo da ke faɗin jihar, domin inganta tsaftar al’ada da rage cikas ga karatunsu.
Arewa Updates ta rawaito cewa, shirin na cikin wani babban shiri mai suna Flow With Confidence, wanda Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar a ƙarƙashin gidauniyar Renewed Hope Initiative.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, an tsara shirin ne domin samar wa ɗalibai mata 10,000 kayan tsaftar al’ada da za su wadace su na tsawon shekara guda, musamman domin rage yawan kwanakin da wasu daga cikinsu ke fasa zuwa makaranta sakamakon rashin samun audugar mata a lokacin al’ada.
A yayin ƙaddamar da shirin, Hajiya Maryam Abba Kabir Yusuf ta kuma gabatar da tallafin kuɗi ga mata sama da 500 a Ƙaramar Hukumar Gwale, domin ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ƙananan sana’o’i da bunƙasa hanyoyin dogaro da kai.
Ta bayyana muhimmancin tallafa wa mata da ɗalibai mata, musamman ta fuskar samar musu da abubuwan da za su taimaka wajen inganta rayuwarsu da samun damar cin moriyar ilimi.
Uwargidan Gwamnan ta kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su haɗa kai wajen tallafa wa irin waɗannan shirye-shirye, domin bunƙasa ilimin ’ya’ya mata da ƙarfafa tattalin arzikin mata da iyalansu.
