Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana damuwarsa kan alkiblar da kasar ke bi yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2027, inda ya yi gargadin cewa karuwar rashin hakuri da ra’ayin siyasa, tashin hankali da rikicin kabilanci na iya kawo barazana ga zaman lafiya da hadin kan kasa.
Jonathan ya ce yadda ake gudanar da kamfen din siyasa a yanzu ya fara kama da na ayyukan kungiyoyin asiri, inda ya ce wasu ‘yan siyasa ke nuna rashin amincewa da ra’ayin wadanda ba sa tare da su, ko kuma su mutunta hakkinsu na neman mulki.
Daily Trust ta rawaito cewa Jonathan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja, yayin wani taron zaman lafiya da tsaro da gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya.
Jonathan ya ce ya a ci gaba da samun kiraye-kiraye daga ‘yan Najeriya da kawayen ta daga sassa daban-daban nanduniya, wadanda ke nuna damuwarsu kan yanayin siyasar kasar gabanin zaben 2027.
Ya ce maimakon a samu kwarin gwiwa da fata na alheri, mutane na kara fargabar yiwuwar barkewar rikice-rikice bayan zaben, don haka bai kamata a yi watsi da wannan damuwa ba.
