Thursday, November 19, 2026
HomeLabaraiASUU Ta Fara Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani a Jami’ar Jihar...

ASUU Ta Fara Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani a Jami’ar Jihar Zamfara

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Zamfara, ta ayyana yajin aikin sai baba ta gani bisa zargin gwamnatin jihar da ƙin biyan buƙatunta.

Buƙatun ƙungiyar sun haɗa da aiwatar da yarjejeniyar albashi da gwamnatin tarayya ta kulla da ASUU a watan Disamban 2025, da kuma biyan basussukan alawus-alawus da haƙƙoƙin malamai.

Mukaddashin shugaban reshen ƙungiyar, Anas Abubakar Dogo, ne ya bayyana hakan bayan wani taron ƙungiyar da aka gudanar ranar Talata a harabar wucin-gadin jami’ar da ke Talata Mafara.

Ya zargi gwamnatin jihar da gazawa wajen magance matsalolin da malaman jami’ar ke fuskanta, duk da ƙoƙarin da ƙungiyar ta yi na tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa.

Dogo ya ce matakin ya biyo bayan ƙarewar wa’adin da ƙungiyar ta bai wa gwamnati, da kuma yajin aikin gargaɗi na mako guda da ta fara ranar 11 ga Nuwamban 2026, ba tare da samun wani sakamako mai kyau ba.

Ya bayyana cewa ƙungiyar ta gudanar da tarurruka da majalisar gudanarwar jami’ar da shugabanninta, tare da ƙoƙarin ganawa da kwamishinan ilimi, shugaban ma’aikatan gwamnati da sakataren gwamnatin jihar, amma hakan bai haifar da ɗa mai ido ba.

Ya ce, “Mun yi amfani da duk hanyoyin tattaunawa da suka dace, amma abin takaici ba a samu wani gagarumin mataki kan buƙatunmu ba.”

Ƙungiyar ta buƙaci ɗalibai, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki da su shiga tsakani domin ganin an warware rikicin, tana mai cewa ba ta da wani zaɓi illa janye ayyukanta har sai gwamnati ta biya buƙatunta.

Ana sa ran yajin aikin zai kawo tsaiko ga karatun ɗalibai a jami’ar har sai an cimma matsaya tsakanin malaman da gwamnatin jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments