Thursday, November 19, 2026
HomeLabaraiMusulmai Za Su Zarta Kiristoci Yawan Jama’a a Duniya Nan Da 2035

Musulmai Za Su Zarta Kiristoci Yawan Jama’a a Duniya Nan Da 2035

Wani sabon rahoton Cibiyar Bincike ta Pew Research Center ya yi hasashen cewa Musulmai za su zarta Kiristoci wajen yawan mabiya a duniya nan da shekarar 2035, sakamakon saurin ƙaruwar al’ummar Musulmi.

Rahoton TRT Afrika ya nuna cewa, adadin Musulmai a duniya zai ƙaru da kusan kashi 80 cikin 100 tsakanin shekarar 2020 zuwa 2070, inda ake hasashen za su kai sama da biliyan 3.6, yayin da Kiristoci za su kasance ƙasa da biliyan 3.

A cewar rahoton, Musulmai za su kai kashi 36 cikin 100 na al’ummar duniya nan da shekarar 2070, idan aka kwatanta da kashi 26 cikin 100 a shekarar 2020. Yayin da ake hasashen kaso na Kiristoci zai tsaya a kusan kashi 29 cikin 100.

Cibiyar Pew ta danganta wannan ƙaruwar da yawan haihuwa da kuma ƙarancin shekarun Musulmai idan aka kwatanta da sauran al’ummomi.

Rahoton ya nuna cewa tsakanin shekarar 2020 zuwa 2025, matsakaicin adadin yaran da mace Musulma ke haifa ya kai 3.1, yayin da na matan da ba Musulmai ba ya kasance 2.0.

Haka kuma, matsakaicin shekarun Musulmai a shekarar 2020 ya kasance 24, yayin da na waɗanda ba Musulmai ba ya kai shekara 33.

Rahoton ya kuma yi hasashen cewa Pakistan za ta zama ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan Musulmai a duniya nan da shekarar 2070, sai Indiya, Nijeriya da Indonesiya.

Haka kuma, ana sa ran Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo za ta zarta Amurka wajen yawan Kiristoci a wannan lokaci.

Sai dai cibiyar ta bayyana cewa hasashen ya dogara ne kan ci gaba da kasancewar yanayin haihuwa, sauya addini da ƙaura kamar yadda aka gani a baya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments