Thursday, November 19, 2026
HomeLabaraiSojoji Sun Kama Matashin Da Ya Yi Karyar Shi Ɗan Sandan Rakiyar...

Sojoji Sun Kama Matashin Da Ya Yi Karyar Shi Ɗan Sandan Rakiyar Motar Dangote ne a Filato

Dakarun rundunar Operation ENDURING PEACE sun kama wani matashi mai shekara 23 da ya yi ikirarin cewa shi ɗan sandan rakiyar kaya ne, bayan direban wata babbar motar kamfanin Dangote ya tsere ya bar motar a jihar Filato.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Talata, 17 ga Nuwamba, 2026, a shingen binciken sojoji na Babale da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin sun tsayar da motar mai lambar rajista Kano FGE-620ZY da misalin ƙarfe 3:49 na dare domin gudanar da binciken tsaro, amma direban ya tsere bayan ya yi watsi da motar, inda ya bar wani mutum a cikinta.

Sojojin sun cafke mutumin da aka gano da suna Gadafi Sani, mai shekara 23, wanda ya bayyana kansa a matsayin ɗan sandan da aka ɗora wa alhakin rakiyar motar.

Sai dai bayan ya kasa gabatar da katin shaidar ɗan sanda ko wata takardar da za ta tabbatar da matsayinsa, hakan ya ƙara jawo zargi game da ikirarinsa.

A halin yanzu, an tsare matashin tare da motar da aka kwato, yayin da ake gudanar da bincike domin gano dalilin tserewar direban, sahihancin ikirarin wanda aka kama da kuma manufar tafiyar motar.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Operation ENDURING PEACE ke ƙara tsaurara binciken ababen hawa da sa ido a manyan hanyoyin sufuri domin dakile ayyukan laifi a jihar Filato.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments