Wasu masu zanga-zanga a Afirka ta Kudu sun bukaci gwamnatin ƙasar ta haramta wa ’yan Najeriya shiga ƙasar, tare da rufe iyakokinta ga ’yan ƙasar.
Daily Trust ta ruwaito cewa, masu zanga-zangar, waɗanda ke ƙarƙashin ƙungiyar March and March, sun gudanar da zanga-zangar ne a birnin Pretoria, inda suka zargi ’yan Najeriya da hannu wajen safarar miyagun ƙwayoyi da haddasa matsalolin zamantakewa.
Jagororin zanga-zangar, ƙarƙashin Jacinta Ngobese-Zuma, sun gudanar da gangamin a unguwar Sunnyside da ake kira Little Lagos saboda yawan ’yan Najeriya da ke zaune a yankin.
Lauyan ƙungiyar, Xolani Zuma, ya bukaci gwamnatin Afirka ta Kudu ta haramta wa ’yan Najeriya shiga ƙasar, yana mai zargin wasu daga cikinsu da safarar miyagun ƙwayoyi.
Haka kuma, masu zanga-zangar sun bukaci a tsaurara dokokin shige da fice, a takaita karɓar ‘yan gudun hijira tare da gaggauta korar baƙin haure da ba su da takardun zama a ƙasar.
Sun kuma nemi Afirka ta Kudu ta fice daga yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya ta shekarar 1951 da ta shafi kare haƙƙin ‘yan gudun hijira.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun takun-saƙa tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu kan hare-haren ƙyamar baƙi da ake kai wa ‘yan Najeriya.
A makon da ya gabata ma, an samu saɓani tsakanin Babban Jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, Femi Fani-Kayode, da fadar shugaban ƙasar, kan cire jawabin da ya shirya gabatarwa yayin miƙa takardun shaidar jakadancinsa.
Sai dai Fani-Kayode ya ce an warware saɓanin bayan Shugaba Cyril Ramaphosa ya shiga tsakani, inda ya kuma yi gargaɗin cewa Najeriya ba za ta yi watsi da ‘yan ƙasarta da ke fuskantar hare-haren ƙyamar baƙi ba.
