Friday, November 20, 2026
HomeLabaraiMutane 14 Sun Mutu a Wani Hatsarin Mota a Jihar Neja

Mutane 14 Sun Mutu a Wani Hatsarin Mota a Jihar Neja

Akalla mutane 14 ne suka mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da wata babbar mota da ke ɗauke da fasinjoji da shanu 35 a kan hanyar Kontagora da ke Jihar Neja.

Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe ranar 17 ga Nuwamba, 2026, a kusa da garin Ibeto, lokacin da motar mai lambar rajista Lagos AZL 267 XH ke kan hanyarta daga Ƙaramar Hukumar Koko ta Jihar Kebbi zuwa Legas.

Rahoton ya nuna cewa hatsarin ya faru ne bayan wata mota da ba a tantance ba ta yi ƙoƙarin wuce babbar motar, inda ta goge ta, lamarin da ya sa direban ya rasa iko da motar ta faɗi.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Direban babbar motar da wasu fasinjoji 13 sun mutu nan take, yayin da aka gano gawarwakin biyu da ba a tantance su ba a ajiye su a ɗakin ajiyar gawa na Babban Asibitin Kontagora.

An ce an miƙa gawarwakin da ‘yan uwansu suka gane domin binne su bisa tsarin addinin Musulunci.

Rahoton ya ƙara da cewa an gano motar da ake zargin ta haddasa hatsarin a Kaboji, cikin Ƙaramar Hukumar Magama, inda aka kai ta ofishin rundunar ‘yan sanda ta Area Command, amma direbanta ya tsere.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja ta tabbatar da cewa tana gudanar da bincike domin gano cikakken abin da ya haddasa hatsarin da kuma kamo direban da ya tsere.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments