Saturday, November 21, 2026
HomeLabaraiRarara Ya Sha Da Ƙyar Bayan Wasu Matasa Sun Yi Ƙoƙarin Farmakarsa...

Rarara Ya Sha Da Ƙyar Bayan Wasu Matasa Sun Yi Ƙoƙarin Farmakarsa a Abuja

Fitaccen mawaƙin siyasar Najeriya, Dauda Kahutu Rarara, ya tsallake farmakin wasu matasa da suka yi yunƙurin lakada masa duka a Babban Masallacin Juma’a na Abuja.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan kammala sallar Juma’a, inda matasan suka yi yunƙurin kai masa hari, lamarin da ya haddasa hayaniya a harabar masallacin.

Sai dai jami’an tsaro sun yi gaggawar shiga tsakani tare da kuɓutar da mawaƙin daga hannun matasan, kafin su fitar da shi daga wurin domin kare lafiyarsa.

Wasu bidiyoyi da suka yaɗu a kafafen sada zumunta sun nuna yadda matasan suka yi yunƙurin farmakar Rarara, yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin shawo kan lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments