Fitaccen ɗan siyasar adawa, Alhaji Buba Galadima, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa zargin yin watsi da yaran da aka sace daga wasu al’ummomi a Jihar Borno.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Galadima ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da ƙungiyar Nigeria Democratic Coalition (NDC) ta shirya a Maiduguri ranar Juma’a.
Ya ce yadda gwamnatin tarayya ta yi shiru kan sace yaran da aka yi a al’ummomin Mussa da Lassa, ya nuna cewa gwamnatin Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, ta yi watsi da al’ummar Borno.
Ya kwatanta lamarin da sace wasu yara da aka yi a Jihar Oyo, inda ya yi zargin cewa Shugaba Tinubu ya tura manyan jami’an tsaro daga sassa daban-daban na ƙasar domin ceto yaran.
A cewarsa, duk da cewa Borno ce mahaifar mataimakin shugaban ƙasa, gwamnatin tarayya ba ta nuna irin wannan ƙoƙari wajen ceto yaran jihar ba.
Galadima ya ce: “Mahaukaci tsagwaran ne kaɗai zai zaɓi Tinubu a Borno.”
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakan ceto yaran da aka sace, yana mai gargadin cewa ci gaba da yin shiru kan lamarin zai ƙara nuna wariya ga Borno da sauran yankin Arewa maso Gabas.
Taron dai na da manufar wayar da kan al’umma da neman goyon baya ga tikitin takarar shugaban ƙasa na haɗin gwiwa tsakanin NDC da Peter Obi.
