Ana fargabar mutane da dama sun mutu bayan wani kwale-kwale da ke ɗauke da fasinjoji ya kife a Jihar Bayelsa da ke kudancin Nijeriya.
Lamarin ya faru ne a kusa da garin Ukubie, cikin ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu, yayin da fasinjojin ke kan hanyarsu ta zuwa jana’iza.
Wata shaidar gani da ido, Sophie Igoniwari, ta ce kwale-kwalen ya cika maƙil sakamakon turereniyar da aka yi yayin shiga cikinsa a garin Anyama Ijaw.
Ta bayyana cewa an ga an fitar da wasu daga cikin mutanen zuwa gabar ruwa bayan kwale-kwalen ya kife jim kaɗan da tashinsa.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Musa Mohammed, ya tabbatar da cewa an tura jami’an rundunar ’yan sandan ruwa domin taimakawa ayyukan ceto.
Sai dai har zuwa lokacin fitar da rahoton, hukumomi ba su bayyana adadin waɗanda suka mutu, waɗanda aka ceto ko kuma waɗanda ake nema ba.
Hatsarin kwale-kwale dai na yawan faruwa a wasu sassan Nijeriya, musamman sakamakon cunkoso da rashin bin ƙa’idojin tsaro a hanyoyin ruwa.
