Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC) ta lalata jabun magunguna da sauran kayayyaki da wa’adin amfani da su ya ƙare ko aka haramta amfani da su, waɗanda kuɗinsu ya kai Naira biliyan 100.
Daraktar Janar ta hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ta ce an gudanar da aikin lalata kayayyakin a Ogwama Dumpsite da ke Ogere Remo, Jihar Ogun.
Ta ce kayayyakin da aka lalata sun haɗa da jabun magunguna, waɗanda wa’adin amfani da su ya ƙare , magungunan da ba su da rajista, allurar Analgin da aka haramta, maganin tari mai ɗauke da Codeine da jabun kayan kwalliya.
Haka kuma, hukumar ta kwace kwalaye sama da 100,000 na barasa da aka haramta sayarwa a cikin leda da ƙananan kwalaben roba a jihohin Lagos da Ogun.
Adeyeye ta ce jami’an hukumar sun kuma gano wasu wuraren da ake ƙera jabun barasa da kayan kwalliya, tare da sake sanya wa wasu abubuwan sha da suka ƙare wa’adinsu sabbin bayanan ƙarewar amfani.
Ta ƙara da cewa an kama waɗanda ake zargi da hannu a harkokin, kuma za su fuskanci hukunci bisa doka.
Daraktar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji sayen magunguna daga wuraren da ba su da izini, tare da bai wa hukumar bayanan da za su taimaka wajen yaƙi da jabun magunguna da kayayyaki masu illa ga lafiyar al’umma.
