Sunday, November 22, 2026
HomeLabarai'Yan Bindiga Sun Ƙóna Ƙauye, Sun Hallaka Hakimi Da Wasu Mutane a...

‘Yan Bindiga Sun Ƙóna Ƙauye, Sun Hallaka Hakimi Da Wasu Mutane a Jihar Neja

Wasu ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Lumma Ba’are da ke ƙaramar hukumar Borgu a Jihar Neja, inda suka kashe hakimin ƙauyen, Mallam Garba, tare da wasu mazauna yankin.

Wata majiya daga cikin al’umma ta bayyana cewa maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 6:00 na safiyar ranar Asabar, inda suka ƙona gidaje da shaguna tare da sace wasu mutanen ƙauyen da kuma satar shanu.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Majiyar ta ce maharan sun kashe hakimin ƙauyen, inda suka jefa gawarsa cikin wutar da suka kunna.

Haka kuma, rahoton ya bayyana cewa wasu mayaƙan sa-kai na Kambari sun kai harin ramuwar gayya a ƙauyen Wawa da misalin ƙarfe 3:00 na yamma, inda suka farmaki Fulani mazauna yankin tare da kashe wasu da jikkata wasu.

Majiyar ta ce harin ya shafi mata, yara, tsofaffi da jarirai, yayin da ake kai waɗanda suka jikkata asibitoci domin neman agajin gaggawa.

Sai dai kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da harin da aka kai Lumma Ba’are, inda ya ce mutane biyar ne aka tabbatar sun mutu.

Ya ƙara da cewa an tura jami’an tsaro haɗin gwiwa zuwa yankin domin shawo kan lamarin da kuma kamo waɗanda ake zargi da kai harin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments