Ma’aikatar tsaron Najeriya ta goge wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X kan taron gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC mai mulki, bayan fuskantar suka daga ’yan Najeriya.
Saƙon da aka wallafa ya bayyana cewa ministan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya kai ziyara wajen da aka gudanar da gangamin domin duba shirye-shiryen tsaro kafin taron.
Sai dai wallafar ta janyo ce-ce-ku-ce, inda wasu ’yan Najeriya suka zargi ministan da amfani da muƙaminsa wajen harkokin siyasa, maimakon mayar da hankali kan matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar.
Wasu masu amfani da kafar X sun nuna damuwa kan yadda ministan ke halartar ayyukan siyasa, duk da matsalolin ’yan bindiga da ta’addanci da ke addabar sassan ƙasar.
Sun kuma bayyana cewa Ma’aikatar Tsaro da rundunonin soji na ƙasa ne baki ɗaya, ba na wata jam’iyya ko ɗan siyasa ba.
Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu da manyan jiga-jigan APC sun halarci gangamin jam’iyyar a ranar Asabar, inda ya yi kira ga al’umma su ci gaba da mara wa APC baya.
A yayin taron, Tinubu ya kuma yi alƙawarin inganta samar da wutar lantarki a ƙasar, yana mai cewa Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, na ƙoƙarin ganin an samu ci gaba a fannin.
