Wednesday, November 25, 2026
HomeLabaraiAtiku Ya Yi Alƙawarin Farfaɗo da Kamfanin Ajaokuta Tare da Gina Tashar...

Atiku Ya Yi Alƙawarin Farfaɗo da Kamfanin Ajaokuta Tare da Gina Tashar Jiragen Ruwa ta Idah

Ɗantakarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin farfaɗo da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta tare da bunƙasa tashar jiragen ruwa ta Idah da ke jihar Kogi idan aka zaɓe shi a 2027.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin ziyarar yaƙin neman zaɓensa a Lokoja, babban birnin jihar Kogi, ranar Talata.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da sake fara aiki a kamfanin Ajaokuta mai kusan shekaru 50, domin samar da ayyukan yi da bunƙasa masana’antu.

Ya kuma yi alƙawarin inganta hanyoyi da samar da ruwan sha a gabashin Kogi, tare da kammala hanyar Kabba zuwa Egbe da ke yammacin jihar.

Atiku ya ce bunƙasa tashar jiragen ruwa ta Idah zai taimaka wa manoma da ’yan kasuwa wajen kai hajarsu ga abokan ciniki cikin sauƙi.

Ya ƙara da cewa al’ummar Kogi sun cancanci gwamnati da za ta mayar da albarkatun jihar zuwa ayyukan yi, ingantattun ababen more rayuwa da inganta rayuwar jama’a.

Kamfanin ƙarafa na Ajaokuta dai wanda aka fara tun shekarun 1970, ya shafe shekaru da dama ba tare da fara cikakken aiki ba, sakamakon matsalolin shari’a, ƙarancin kayan masarufi da sauye-sauyen manufofin gwamnatoci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments