Wednesday, November 25, 2026
HomeLabaraiMasarautar Gumel Ta Hana Ɗaukar Hotuna Da Bidiyo Ba Tare Da Izini...

Masarautar Gumel Ta Hana Ɗaukar Hotuna Da Bidiyo Ba Tare Da Izini Ba

Masarautar Gumel da ke Jihar Jigawa ta haramta ɗaukar hotuna da bidiyo, da kuma tattarawa ko yaɗa bayanan da suka shafi harkokin cikin masarautar ba tare da izinin fadar ba.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Majalisar Masarautar, Alhaji Murtala Aliyu, ya fitar, kamar yadda Arewa Updates ta rawaito.

Sanarwar ta bayyana cewa, mutanen da ba sa cikin jami’an yaɗa labaran da fadar masarautar ta amince da su ba su da izinin ɗaukar hotuna ko bidiyo, ko tattara bayanai da sunan wakiltar masarautar ba tare da sahalewar fadar ba.

Haka kuma, masarautar ta haramta amfani da sunanta wajen fitar da sanarwa ko wallafa rahotanni ba tare da samun izini daga hukumomin fadar ba.

Baya ga haka, sanarwar ta ce an haramta ƙirƙirar shafukan sada zumunta da sunaye ko alamomin da suka danganci masarautar ba tare da amincewar fadar ba.

Fadar masarautar ta gargaɗi duk wanda ya saɓa wa waɗannan ƙa’idoji cewa za ta ɗauki matakan da suka dace a kansa bisa tanadin doka.

Sai dai sanarwar ta fayyace cewa, babu wata matsala wajen sake yaɗa sanarwar da ta fito daga sahihan majiyoyin da masarautar ta amince da su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments