Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta kama mutane uku bisa zargin hannu a rikicin siyasa da ya ɓarke a Zauro, Makera da wasu yankuna na ƙaramar hukumar Birnin Kebbi.
Rundunar ta ce rikicin ya faru ne yayin wani taron siyasa da aka gabatar da shi a matsayin rabon kayan tallafi, wanda matar ɗan takarar gwamnan ADC ta shirya a Zauro, Makera, Gwadangwaji, Gawasu, Morida da Karyo.
A cewar rundunar, masu shirya taron sun karya yarjejeniyar da aka cimma da jam’iyyun siyasa, wadda ta wajabta sanar da ’yan sanda aƙalla sa’o’i 48 kafin gudanar da duk wani taron siyasa.
’Yan sanda sun ce sun samu bidiyoyin da ke nuna wasu mutane a cikin ayarin taron ɗauke da sanduna, adduna da takubba, yayin da wasu masu jawabi suka yi kalaman da ka iya tayar da tarzoma.
Haka kuma, an ga wasu motoci ba tare da lambobin rajista ba ko kuma da lambobin da ake zargi, tare da amfani da sirens ba bisa ƙa’ida ba.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Rundunar ta bayyana cewa an gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu, tare da gargaɗin cewa ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na tada zaune tsaye ko amfani da matasa wajen tashin hankali na siyasa ba.
Ta kuma ce an dakatar da wani taron siyasa da aka shirya a Jega saboda rashin sanar da ’yan sanda, inda aka umarci masu shirya shi su sake tsara lokacin tare da sanar da rundunar domin samar da tsaro.
Rundunar ta buƙaci iyaye da masu kula da yara su hana amfani da su wajen harkokin siyasa da ka iya jefa su cikin tashin hankali, tana mai cewa duk wanda aka samu da hannu wajen tayar da zaune tsaye ko ɗaukar nauyin ’yan daba zai fuskanci hukunci bisa doka.
