Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zai ƙaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a ƙananan hukumomi 44 na jihar, a ranar Lahadi, 29 ga Nuwamba, 2026.
Kwamishinan yaɗa labarai, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Ya ce za a fara gangamin ne a ƙaramar hukumar Rogo saboda muhimmancin matsayinta na garin da ke kan iyakar jihar.
Gwamnan ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki su guji duk wani abu da zai kawo tashin hankali, musamman nuna ko daukar makamai yayin gudanar da gangamin.
Haka kuma, ya buƙaci masu ababen hawa su kiyaye dokokin hanya domin kauce wa haɗurra a lokacin gudanar da tarukan.
Sanarwar ta ƙara da cewa a kowace ƙaramar hukuma da gwamnan zai ziyarta, za a ƙaddamar da wasu ayyukan gwamnati, duba waɗanda ake gudanarwa ko aza harsashin sababbi.
A cewar sanarwar, gangamin zai ba gwamnan damar tattaunawa kai tsaye da al’ummar ƙananan hukumomi 44, tare da bayyana nasarorin gwamnatinsa.
