HomeSashen HausaƊaliban Katsina Za Su Koma Makaranta Daga 28 ga Watan Disamba– Gwamnatin...

Ɗaliban Katsina Za Su Koma Makaranta Daga 28 ga Watan Disamba– Gwamnatin Jiha ‎

-

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da ranakun komawar daliban makarantun sakandare domin fara zangon karatu na biyu na shekarar 2025/2026, tare da bayyana jadawalin jarabawa da rajistar WASSCE.

‎A wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta jihar ta fitar ranar 23 ga watan Disamba, 2025, ta ce daliban makarantun sakandare na kwana (boarding) za su koma makaranta a ranar Lahadi, 28 watan ga Disamba, 2025.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, ‎Sanarwar ta bayyana cewa, umarnin ya shafi dukkan makarantun sakandare na kwana a fadin jihar, ciki har da Unity Secondary School da ke Malumfashi da Jibia, inda aka ce dalibai masu musayar karatu ma na a cikin shirin.

‎Sai dai daliban da ke zuwa makarantar jeka-ka-dawo (day students) za su koma ne a ranar 11 ga watan Janairu, 2026.

‎Haka kuma, ma’aikatar ta ce jarabawar ƙarshen zangon karatuna farko za ta fara ne daga ranar Litinin, 29 ga watan Disamba, 2025, a dukkan makarantun sakandare na kwana.

Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar ya fitar, Sani Danjuma Suleiman, a ranar Talata 23 ga watan Disamba 2025, ɗauke da sa-hannunsa.

‎Game da jarabawar kammala sakandare kuwa, sanarwar ta ce daliban aji na uku (SS III) za su yi rajistar WASSCE ta zahiri (offline) daga 28 zuwa 31 ga watan Disamba, 2025, inda aka gargade su da su tabbatar da sun yi rajistar domin guje wa maimaita shekarar karatu.

‎Daga Karshe ma’aikatar ta shawarci iyaye, masu kula da dalibai da shugabannin makarantu da su kula da wadannan ranaku tare da tabbatar da bin umarnin yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎Gwamnan Plateau Ya Kaddamar Da Jami,’an Tsaro 1,450 Na Operation Rainbow

Gwamnan Jihar Plateau, Barrista Caleb Manasseh Mutfwang, a ranar Talata ya kaddamar da jami'an tsaro 1,450 da aka kammala horaswa a karkashin shirin Operation Rainbow,...

‎APC Ta Shirya Karɓar Gwamnan Plateau a Wata Mai Zuwa

‎Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta tabbatar da shirinta na karɓar Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, a wata mai zuwa, lamarin da ya fara jawo...

Most Popular