HomeSashen Hausa‎Gwamnatin Tarayya ta Kammala Horas da Sama da Jami’an Tsaron Daji 7,000...

‎Gwamnatin Tarayya ta Kammala Horas da Sama da Jami’an Tsaron Daji 7,000 a Jihohi 7

-

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce ta kammala horas da sama da sabbin jami’an tsaron daji 7,000 da aka dauka aiki daga jihohi bakwai, a wani yunkuri na kara karfafa matakan tsaro a yankunan dazuka da ke fama da barazanar tsaro.

‎Jami’an sun samu kammala horo na tsawon watanni uku karkashin shirin da ake kira Presidential Forest Guards Initiative, wanda aka kirkira domin dakile ayyukan ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran kungiyoyin masu aikata laifuka da ke fakewa a cikin dazuka.

‎Mahukunta sun bayyana cewa horon ya mayar da hankali ne kan dabarun tsaron daji, tattara bayanan sirri, sa ido a yankunan karkara, da kuma yadda jami’an za su yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro na kasa.

‎Gwamnatin Tarayya ta ce an zabi jihohin da suka ci gajiyar shirin ne bisa la’akari da yadda suke fuskantar kalubalen tsaro, musamman a yankunan dake da manyan dazuka.

‎A cewar gwamnati, an tanadi tura wadannan jami’ai ne zuwa jihohinsu domin fara aiki, tare da samar musu da kayan aiki wanda suka dace da kuma yin tsarin hada kai da ‘yan sanda da sojoji.

‎Wasu masana harkokin tsaro na ganin cewa shirin na iya taimakawa wajen rage matsalolin tsaro a yankunan karkara, amma suna jan hankali kan muhimmancin kula da jin dadin jami’an da kuma tabbatar da sa ido kan aikinsu.

‎Gwamnatin Tarayya ta ce shirin dai, zai ci gaba da fadada ne zuwa wasu karin jihohin a nan gaba, a matsayin wani bangare na kokarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎DA DUMI-DUMI: Rikici Ya Ɓarke A Sabuwar Unguwa Katsina, Mutum 1 Ya Rasu, Matasa Sun Cinna Wuta a Ofisoshin Tsaro

‎A daren jiya zuwa safiyar yau, an samu tashin hankali a Sabuwar Unguwar Kofar Kaura, lamarin da ya janyo hankalin al’umma tare da haifar da...

‎Kwankwaso Ya Bayyana Wadanda Zasu Yi Takarar Zaben Cike Gurbi A Jam’iyyar NNPP

Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya amince da bai wa ’ya’yan ’yan Majalisar Jiha biyu da suka rasu, damar tsayawa takara, domin neman...

Most Popular