A daren jiya zuwa safiyar yau, an samu tashin hankali a Sabuwar Unguwar Kofar Kaura, lamarin da ya janyo hankalin al’umma tare da haifar da tambayoyi da dama kan ainihin abin da ya faru.
Rahotannin da kafar Katsina Online ta wallafa a Shafin sada zumunta ya nuna cewa, lamarin ya samo asali ne bayan zuwan jami’an tsaro a unguwar. Wasu shaidu da suka nemi a sakaya sunayensu sun shaida cewa jami’an sun shigo ne domin gudanar da aiki, inda a wata majiyar aka ce gargadi aka zo bayarwa.
A cewar wadannan shaidu, a yayin aikin jami’an ne aka kama wani matashi da ake kira Dan Kuda, wanda rahotanni ke nuna cewa ya yi tirjiya da umarnin jami’an tsaro. Hakan ne, a cewar shaidun, ya haifar da hatsaniya, inda daga bisani matashin ya rasa ransa sakamakon harbin bindiga.
Bayan faruwar lamarin, dattawan unguwar sun yi ƙoƙarin kwantar da tarzoma tun daga daren jiya, tare da kira ga matasa da su yi haƙuri su guji ɗaukar doka a hannunsu.
Sai dai a lokacin jana’izar Dan Kuda, wasu fusatattun matasa sun kai hari kan ofishin Civil Defence da ke kan hanyar zuwa makabarta, inda aka kona wani ɓangare na ofishin tare da wasu babura.
Rahotanni sun kuma nuna cewa bayan kammala jana’izar, matasan sun tunkari ofishin ’yan sanda da ke cikin filin Kanada. A nan ne jami’an tsaro suka yi ƙoƙarin tarwatsa taron ta hanyar amfani da barkonon tsohuwa, lamarin da ya janyo konewar wani sashe na ciyawar makabarta.
Rahoton ya shaida cewar, ya ji karar harbin bindiga, kuma da idonsa ya ga akalla mutane uku da aka harba, sai dai ba a samu cikakken bayani kan halin da suke ciki ba a wannan lokaci.
Haka kuma, ana zargin cewa wani mutum ya rasa ransa sakamakon harbin da aka yi masa bayan kammala jana’izar, kodayake wannan batu na bukatar karin tabbaci daga hukumomin tsaro.
Ya zuwa yanzu dai, babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ’yan sanda ko Civil Defence dangane da lamarin.
Al’ummar yankin na ci gaba da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi, tare da daukar matakan da za su hana sake aukuwar irin wannan tashin hankali.
Za mu ci gaba da bibiyar lamarin, kuma za mu kawo muku ƙarin bayani da zarar mun samu cikakken rahoto daga bangarorin da abin ya shafa.
