HomeSashen HausaSAKON ƘARSHEN SHEKARA NA KATSINA TIMES: Mun Fuskanci Barazana Da Kalubale A...

SAKON ƘARSHEN SHEKARA NA KATSINA TIMES: Mun Fuskanci Barazana Da Kalubale A Shekarar 2025– Inji Malam Muhammad Danjuma Katsina

-

Tunda farko, ya yi godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki, tare da salati da aminci ga Manzon Rahama, Annabi Muhammad (SAW), iyalansa (AS) da sahabbansa (RA), bisa ni’imar da ya yi mana ta kai mu ƙarshen shekarar 2025 cikin koshin lafiya.

 

Ya kuma roƙi Allah ya kare su, ya ba su nasara da sa’a a shekarar 2026 da ke tafe.

 

Haka kuma, ya nemi gafarar Ubangiji bisa kura-kuran da suka aikata a shekarar 2025, tare da neman afuwar jama’a bisa duk wani rashin jin daɗi da ka iya faruwa sakamakon wasu rahotanni ko binciken labarai da suka wallafa a shekarar da ta gabata.

 

A cewar sa, a shekarar 2025, sun samu nasarori daban-daban, waɗanda za su riƙa kawo su dalla-dalla a nan gaba.

Sai dai kuma, sun fuskanci ƙalubale iri-iri. Daga cikinsu akwai barazanar kotu har guda 19, tare da takardun jiran kiran kotu guda 5, dukkaninsu suna da alaƙa da salon rahotanninsu ko binciken labaransu.

 

Ya ƙara da cewa, ya fuskanci barazanar kai tsaye har guda 6, amma bisa kiyayewar Allah, babu abin da ya faru.

 

Ya yi nuni da cewa, a shekarar 2025, ba su fuskanci wata barazana ko tsangwama daga gwamnatin jihar Katsina ko Gwamna ba, ko sau ɗaya.

 

Tuni ya jinjina wa mai Girma Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, PhD, bi sa fahimtarsa da mutunta ‘yancin aikin jarida.

 

Ya yi ƙarin haske da cewa, a iya saninsu, babu wani ɗan jarida da gwamnatin jihar ta sa aka tsare ko aka yi wa barazana a shekarar 2025. Haka kuma, babu wani ɗan kafar sada zumunta (Social Media) da aka ƙuntata ma sa ko aka yi masa barazana bi sa ra’ayinsa.

 

Ya ƙara yaba wa Gwamnan Katsina bi sa cika cikakken tsari na mulkin Dimokiraɗiyya, inda ya amince da cewa ya yarda aikin jarida ya riƙa nuna inda aka yi kuskure, domin gyara da inganta shugabanci.

 

A bisa bincikensu, Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na daga cikin gwamnonin da suka fi fitowa kafofin yaɗa labarai suna bayyana kansu da manufofinsu ga al’umma, idan aka kwatanta da yawancin gwamnonin Najeriya.

 

Ya yi kira da fatan manyan ƙungiyoyin kare haƙƙin ‘yan jarida za su ƙara nazari a kan wannan batu, domin jinjina wa gwamnatin Katsina bi sa barin aikin jarida ya gudana cikin cikakken ‘yanci a jihar.

 

Ya kuma yi hasashen cewa, shekarar 2026 na zuwa ne a matsayin shekara mai zafi a siyasar Nijeriya, kasancewar ita ce shekarar shirye-shiryen zaɓen 2027.

 

Duk da haka ya ce a Katsina Times, sun shirya tsaf don fuskantar wannan ƙalubale, ya ce za su kawo labarai yadda suke, mu fitar da binciken labarai bayan tabbatar da sahihancinsu, tare da wallafa bidiyo, hotuna ko sauti kamar yadda muka same su, bayan cikakken tantancewa.

 

Haka kuma, za su yi sharhi ga duk wani ɗan takara da ke neman wakiltar jama’a, domin ba wa al’umma damar tantancewa, tare da wayar da kan jama’a da su karɓi kyauta, amma su zaɓi wanda ya fi amfani da amana.

 

Ya nanata cewa, a shekarar 2025, sun gudanar da bincike daban-daban; wasu sun dakatar da rahotanninsu sakamakon rashin tabbas a wasu bayanai, yayin da wasu kuma suka kammala su, ya ce suna jiran lokacin da ya dace mu fitar da su, musamman waɗanda suka shafi wasu mutane ko hukumomi.

 

Ya jaddada cewa, ba sa sakin kowanne bincike sai sun tabbatar cewa, suna da hujjoji masu ƙarfi da za su iya kare kansu da su a kowace hukuma ko kotu.

 

Ya Kafa hujjoji da cewa, suna da tsari na sirri da ke kare masu ba su bayanai (sources), kuma ko da ana fuskantar matsin lamba, sun ƙarfafa wannan tsari yadda ya kamata.

 

Ya yi alƙawarin cewa, kamar yadda suka samu cikakken goyon bayan al’umma a shekarar 2025, in sha Allah za su ci gaba da riƙe wannan amana a shekarar 2026.

 

Ya kuma miƙa godiya ta musamman ga abokan hulɗarsu da masu ƙarfafa gwiwa. Haka kuma, ya gode wa tsohon Gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. (Dr.) Aminu Bello Masari, CFR, Dallatun Katsina, tare da hukumar TETFund, bi sa gudummawa da goyon bayan da suka bayar.

 

Muhammad Ɗanjuma,

Shugaban kamfanin Matasa Media Links Ltd,

Masu buga mujallar Katsina City News, Jaridar yanar gizo ta Katsina Times, da shafin jaridar Taskar Labarai.

Fejin mu na Facebook shi ne Katsina City News

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Obi Na Shirin Shiga ADC Yayin Da Jam’iyyar Za Ta Yi Babban Taron Ta Na Ƙasa a 2026

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party (LP), Peter Obi, na dab da shiga jam’iyyar ADC, gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Wata majiya a jam’iyyar...

‎DA DUMI-DUMI: Rikici Ya Ɓarke A Sabuwar Unguwa Katsina, Mutum 1 Ya Rasu, Matasa Sun Cinna Wuta a Ofisoshin Tsaro

‎A daren jiya zuwa safiyar yau, an samu tashin hankali a Sabuwar Unguwar Kofar Kaura, lamarin da ya janyo hankalin al’umma tare da haifar da...

Most Popular