Rundunar ‘Yansanda a jihar Zamfara, a karkashin sashin yaki da masu satar mutane, sun yi nasarar dakile wani hari da ‘yan fashin daji suka kai da ceto mata da yara kanana biyar a kan hanyar Gusau zuwa Dansadau.
Kakakin rundunar ’yan sandan, DSP Yazid Abubakar, ya ce jami’an na sintiri ne lokacin da suka ci karo da ‘yan fashin sun tare motoci, inda aka yi musayar wuta da ta tilasta wa bata-garin tserewa cikin daji da raunukan harbi tare da barin mutanen da suka yi yunkurin sacewa.
Wadanda aka ceto suna tafiya ne daga Wanke zuwa Gusau kafin maharan su yi awon gaba da su.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya tabbatar da cewa an duba lafiyar wadanda aka ceton kuma tuni aka hada su da iyalansu, yayin da ya nanata kudurin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da yin kira ga jama’a da su ci gaba da ba da bayanan sirri ga hukumomi akan lokaci
