Maigirma Gwamna yayi wannan fallasa ne a cikin shirin Sunrise Daily na Channels TV dazu da safe, yace akwai wanda yake shirya min makirci, kuma na san shi, shine Ministan Abuja na yanzu Nyesom Wike, ya fada wa duniya cewa zai kunna wuta a jihata na Bauchi
Kauran Daular Usmaniyyah yaci gaba da cewa; na fahimci Wike ne yake bada umarni wa hukuma irin na EFCC wajen batani, yana bawa mutane cin hanci, yana sayar da filayen Abuja yana amfani dasu wajen cimma burinsa, ba sabon abu bane a gareni saboda na taba rike mukamin Ministan Abuja na shekaru 6 na san komai
Gwamnan Bauchi yaci gaba da cewa; yana da hujjoji daga majiyarsa na sirri dake EFCC wanda suka tabbatar masa da cewa Wike ne yake tsara duk abinda yake faruwa da ‘yan adawar siyasa a Nigeria
Kaura yace tsohon Accountant General dinsa na jihar Bauchi yaci amanata, ni na kaishi Kotu da kaina domin a masa hukunci, daga bisani Kotu ta bada belinsa, to a yanzu Wike ne yake aiki dashi a Kotu wajen bada shaida na karya akan mukarrabaina da aka kama
A matsayina na Gwamna wanda na rike manyan mukamai tun daga Sanata har Minista, ina shugaban al’ummah ta ya zai kasance ina daukar nauyin ta’addanci, ana min wannan sharri ne saboda ina cikin manyan ‘yan adawa
Zan bi duk matakan da suka dace domin na kare kaina, na rubuta wa Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya takardan korafi, tare da sanar da hukumomin tsaro, kuma zan kai korafina zuwa ga hukumonin Majalisar dinkin duniya, inji Maigirma Gwamna
Sannan Gwamna Bala yace Shugaban Kasa Tinubu yana kewaye da ‘yan daba, ‘yan damfara wadanda suke son ha||akashi a siyasance irinsu Wike
Muna rokon Allah Ya kare jihar Bauchi daga wadanda suke neman jingina mana ta’addanci, Allah Ya sa mugun nufinsu ya kare a kansu da iyalansu kadai.
